Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroRudunar Yan sandan Kano ta cafke mutane 47 kan fadan daba da...

Rudunar Yan sandan Kano ta cafke mutane 47 kan fadan daba da wasu zarge-zarge

Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken.

Rundunar ’yan sandan Kano ta ce ta cafke mutane 47 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da daba da safarar miyagun ƙwayoyi.

Rundunar ta ce an gudanar da samamen ne a sassa daban-daban na jihar tsakanin 1 zuwa 7 ga Oktoban 2026, bisa bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar jama’a.

A Panshekara, jami’an tsaro sun gudanar da samame guda uku inda suka cafke mutane 21 tare da kwato wasu nau’o’in miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da Pregabalin, Exol, Diazepam da tabar wiwi.

A Kiru kuma, an cafke wani matashi mai suna Sadam Shuaibu, mai shekaru 22, bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Rundunar ta ce an samu tabar wiwi guda 105 da wasu abubuwa a hannunsa.

A yankin Hotoro Mahautar Gabas, jami’an ’yan sanda sun kama wasu mutane 13 da ake zargi da daba. A yayin samamen, an kwato makamai da suka haɗa da adda, gatari, takubba, wuƙaƙe da sanduna, da kuma wasu abubuwa da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.

Haka kuma, rundunar Anti-Kidnapping Squad ta cafke wasu mutane 10 a yankunan ’Yan Yashi da Kofar Ruwa na ƙaramar hukumar Dala bisa zargin tada hankalin jama’a.

A wani samamen kuma, Special Intervention Squad ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da satar wayoyin hannu a kusa da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano. An ce an kwato wayoyin Android guda uku da kuma keke mai ƙafa uku da ake zargin matasan na amfani da shi wajen aikata laifukan.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce dukkan waɗanda aka kama suna hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike.

Ya ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments