Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamnatin Tarayya za ta rage farashin man fetur a gidajen NNPC na...

Gwamnatin Tarayya za ta rage farashin man fetur a gidajen NNPC na kwanaki 30

Gwamnatin Tarayya ta sanar da bayar da rangwame kan farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen man NNPC na tsawon kwanaki 30, domin rage matsin da tsadar man fetur ke haifarwa ga ’yan Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da bayar da rangwame kan farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen man NNPC na tsawon kwanaki 30, domin rage matsin da tsadar man fetur ke haifarwa ga ’yan Najeriya.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Oyedele ya ce za a ba masu motocin haya da sauran masu jigilar jama’a fifiko a tsarin rangwamen, inda ya jaddada cewa ba wai gwamnati ta dawo da tallafin man fetur ba ne, sai dai za a sayar da man a farashin da ya yi daidai da kudin da aka sayo shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin cimma matsaya kan iyakar farashin saukar man fetur zuwa N1,350 kan kowace lita, tare da duba farashin a kowane wata domin rage sauye-sauyen da farashin man fetur ke samu.

Gwamnatin ta ce matakan na daga cikin kokarinta na rage tasirin tsadar man fetur da sufuri kan al’umma, yayin da ake kuma duba wasu hanyoyin da za su taimaka wajen samar da daidaito a farashin man fetur a nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments