Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da Pa Joseph Iduoriyekemwen, mai shekaru 90, mahaifin ɗan takarar kujerar Majalisar Dattawa ta Edo ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.
An yi garkuwa da dattijon ne daga gidansa da ke Amagba, Benin City, a cikin sa’o’in farko na Talata, 6 ga Oktoban 2026.
Lamarin ya jefa al’ummar Jihar Edo cikin fargaba, musamman yayin da wasu ke nuna zargin cewa satar na iya kasancewa da alaƙa da siyasa.
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani kan yadda aka gudanar da satar ba. Rahotanni sun ce ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da Pa Iduoriyekemwen cikin ƙoshin lafiya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa na Jihar Edo, Kassim Afegbua, ya yi Allah-wadai da satar, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin da “ya saɓa wa ɗabi’a”.
Sai dai Afegbua ya yi gargadin cewa bai kamata a danganta satar da siyasa ba tare da samun kwararan hujjoji ba.
Kwamishinan ya ce abin takaici ne yadda wasu mutane suka yi gaggawar zargin gwamnatin jihar da hannu a satar.
Ya ce irin waɗannan zarge-zarge na iya kawo cikas ga ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar.
Da yake magana kan satar dattijon, Afegbua ya tambaya: “Me zai iya zama dalilin da zai sa wani ya sace irin wannan uba kuma kaka?”
Ya ƙara da cewa Gwamna Monday Okpebholo ya zuba jari mai yawa wajen inganta kayan aikin tsaro a jihar.
A cewarsa, gwamnan ya kuma umarci hukumomin tsaro da su haɗa kai domin tabbatar da an kuɓutar da Pa Iduoriyekemwen cikin gaggawa da ƙoshin lafiya.