Siyasar jihar Edo ta shiga cikin rudani yayin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai hari kan tawagar jam’iyyar ADC a ƙaramar hukumar Igueben.
Lamarin ya faru ne a yammacin Talata, inda aka yi zargin cewa maharan sun buɗe wa tawagar jam’iyyar wuta. Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar, Kenneth Imasuangbon, da ɗan takarar sanatan Edo ta Tsakiya, Herbert Okonofua, na cikin waɗanda suka tsira daga harin, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Sauran shugabannin jam’iyyar da ke cikin ayarin ma sun tsira da ƙyar yayin da ake zargin maharan sun yi musu luguden wuta.
ADC ta zargi wasu masu goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki da hannu a harin, tana mai cewa shugaban ƙaramar hukumar Igueben, Endurance Azemegbe, ne ya jagoranci waɗanda suka kai harin.
Sai dai Azemegbe ya musanta zargin, yana cewa bai ma kasance a Igueben lokacin da lamarin ya faru ba.
Jam’iyyar ADC ta kuma ce wani ɗan goyon bayanta, Jerry Oliha, ya samu raunin harbin bindiga yayin harin. Ta ce an harbe shi a harabar fadar Enogie na Igueben, sannan aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Irrua domin samun kulawar likitoci.
A cewar jam’iyyar, wannan shi ne karo na uku da aka kai wa tawagarta hari a wannan rana, bayan wasu hare-haren harbe-harbe da suka faru a Ward 4 da Ward 5 na ƙaramar hukumar.
ADC ta ce tana kallon hare-haren a matsayin wani ɓangare na abin da ta kira tashin hankali da ake yi wa ‘yan adawa da wuraren jam’iyyar.
Ta kuma yi zargin cewa an samu irin waɗannan hare-hare a ƙananan hukumomin Etsako East, Owan West da Owan East.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ADC na jihar Edo, Chris Ojeikere, ya fitar, jam’iyyar ta ce shugaban Igueben ya jagoranci maharan.
Sanarwar ta ce harin ya rutsa da tawagar Kenneth Imasuangbon da Herbert Okonofua, yayin da Oliha, matashin ɗan jam’iyyar daga Ward 6, ya samu harbin bindiga.
ADC ta ce za ta fitar da cikakken rahoto kan abin da ta bayyana a matsayin siyasar tashin hankali da take zargin APC da gudanarwa. Ta kuma ce an sanar da jami’in ‘yan sanda mai kula da Igueben game da lamarin.
Zargin ya zo ne a lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yanayin siyasar Edo, musamman bayan wasu kalamai da aka danganta ga shugaban APC na jihar, Jarrett Tenebe, inda aka ruwaito yana magana kan amfani da AK-47 wajen fuskantar wasu abokan hamayya a ƙoƙarin samun kuri’u miliyan 2.5.
Sai dai Azemegbe ya ce bai san komai game da harin ba.
Ya ce, “Zan iya tabbatar maka cewa zan binciki lamarin. Ba zan iya magana kan abin da ban sani ba.”
Azemegbe ya ce abin da ya faru ya ba shi mamaki, yana mai cewa mutanen Igueben mutane ne masu zaman lafiya kuma ‘yan’uwa ne.
Shi ma jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Edo, ASP Eno Ikoedem, ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin nan take ba. Ya ce rundunar za ta fara bincike da zarar an kai mata rahoto a hukumance.