Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 ta biya mata albashin baya ko kuma ta fuskanci yajin aikin sai baba-ta-gani.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mohammed Ibrahim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa bayan taron shugabannin SSANU na ƙasa da aka gudanar a Jami’ar Uyo, Akwa Ibom.
Ya ce ƙungiyar na neman a biya dukkan basussukan albashin da suka taso daga sabon tsarin albashi na 2026 FGN/SSANU CONTTA, wanda aka fara aiki da shi tun daga 1 ga Janairu 2026.
SSANU ta kuma nemi a biya ma’aikatan jami’o’i albashin watanni biyu da aka riƙe a lokacin yajin aikin 2022, da kuma bashin ƙarin albashin kashi 25 da 35 cikin 100 na shekara guda.
Ibrahim ya ce jinkirin biyan kuɗaɗen ya ƙara jefa mambobin ƙungiyar cikin matsin tattalin arziki, yana mai cewa waɗannan kuɗaɗe haƙƙoƙinsu ne na halal.
Ya kuma yi kira da a ƙara tallafin jami’o’i domin inganta wutar lantarki, dakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu, ICT, tsaro da sauran ababen more rayuwa.