Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta gayyaci wani ɗan siyasa, Hon. Aminu Abdullahi Warkal, domin yi masa tambayoyi kan zargin nuna bindiga a lokacin wani taron da ake kyautata zaton taron siyasa ne.
Rundunar ta ce ta gano wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ake zargin an ga Warkal yana fito da wata bindiga da ake kyautata zaton bindiga ce kirar pump-action.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Litinin, ya ce idan aka tabbatar da lamarin, hakan na iya saɓa wa tanadin dokar mallakar makamai.
Ya ce irin wannan ɗabi’a na iya “jefa tsoro a zukatan jama’a, tsoratar da al’umma da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron jama’a.”
Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayar da umarnin gayyatar Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai domin yi masa tambayoyi.
Sanarwar ta ce: “Bisa umarnin Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, SFIPMA, MNIM, MNIPS, MASIS, an gayyaci Hon. Aminu Abdullahi Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.”
Rundunar ta ƙara da cewa a halin yanzu Warkal yana hannun sashen leƙen asiri na jihar (SID), inda ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Sai dai ’yan sandan ba su bayyana ko an kwacd bindigar da ake zargin an nuna a bidiyon ba, ko kuma Warkal ya yi wani bayani kan dalilin da ya sa yake da ita ko kuma ya nuna ta.
Rundunar ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci rashin bin doka, daba ko nuna makaman da za su iya barazana ga zaman lafiyar jama’a ba, ba tare da la’akari da matsayin wanda abin ya shafa ba.