Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaINEC: Lagos, Kano da Kaduna sun fi yawan masu rajistar zaɓe

INEC: Lagos, Kano da Kaduna sun fi yawan masu rajistar zaɓe

Jihohin Lagos, Kano da Kaduna ne suka fi yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya gabanin babban zaɓen 2027, a cewar alkaluman Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana alkaluman yayin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar na babban zaɓen 2027.

Lagos ce ke kan gaba da masu rajistar zaɓe 7,488,633, sai Kano da 6,570,276, sannan Kaduna mai 4,662,640.

Katsina ce ke matsayi na huɗu da masu rajista 3,876,051, sai Rivers da 3,736,434, Oyo da 3,588,111, Delta da 3,525,988, Benue da 3,057,225, Ogun da 3,037,981, yayin da Bauchi ke matsayi na 10 da 3,012,547.

Amupitan ya ce alkaluman sun haɗa da bayanan rajistar masu kada ƙuri’a daga matakai uku na aikin rajistar da hukumar ta gudanar.

INEC ta bayyana cewa tana ci gaba da wallafa bayanan masu rajista da sauran ƙididdigar zaɓe domin ƙara fahimtar jama’a game da tsarin zaɓe na ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments