Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa Addis Ababa ta Habasha, inda zai jagoranci tawagar Najeriya wajen tattaunawa kan hanyoyin inganta samar da abinci mai gina jiki.
Shettima ya tafi Habasha ne bisa gayyatar Mataimakin Firaministan ƙasar, Temesgen Tiruneh, domin gudanar da taron farko na musayar kwarewa tsakanin Najeriya da Habasha kan harkokin abinci mai gina jiki.
A yayin ziyarar, tawagar Najeriya za ta musanya kwarewa da hukumomin Habasha kan yadda gwamnati za ta inganta ayyukan abinci mai gina jiki daga matakin tarayya zuwa jihohi da ƙananan hukumomi.
Tawagar za ta kuma ziyarci wasu wurare da suka haɗa da gonar alkama, gonar ayaba da cibiyar horaswa ta ‘Bounty of the Basket’.
Gwamnonin Zamfara da Jigawa, Dauda Lawal da Umar Namadi, da wasu ministoci da jami’an gwamnati, ciki har da Abubakar Atiku Bagudu, Abubakar Kyari da Zubaida Umar Abubakar, na cikin tawagar Shettima.