Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari, ya yi kira ga al’ummar Arewa da su bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas.
Yari ya ce hakan zai nuna girmamawa ga tsarin karɓa-karɓar shugabanci tsakanin yankunan Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin Jihar Kano ranar Asabar, bayan wata ganawar sirri da ya yi da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
A cewarsa, ya kamata Arewa ta nuna dattako tare da mutunta tsarin rabon mulki, sannan ta bai wa Shugaba Tinubu damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas.