Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa2027: Babachir ya fadi abin da Obi da Kwankwaso ke bukatar yi...

2027: Babachir ya fadi abin da Obi da Kwankwaso ke bukatar yi domin samun nasara

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babachir David Lawal, ya shawarci Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso kan matakan da yake ganin za su taimaka musu wajen samun nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Babachir ya bayyana cewa Obi da Kwankwaso ba sa amfani da farin jinin da suke da shi yadda ya kamata, musamman wajen bayyana manufofinsu da shirye-shiryen da suke da su ga jama’a.

A wata hira da aka yi da shi, Babachir ya ce ya taba zama da Peter Obi da Kwankwaso, inda ya shawarce su da su fi mayar da hankali wajen bayyana abin da suke son yi wa kasa maimakon dogaro da yawan magoya baya a taruka.

Da yake magana kan Rabiu Kwankwaso, Babachir ya ce tarukan da ake tara dimbin magoya bayan Kwankwasiyya ba su isa su tabbatar da nasarar dan siyasar ba.

Ya ce ya kamata Kwankwaso ya yi amfani da kwarewarsa a fannin injiniyan ruwa wajen bayyana yadda zai magance matsalolin ruwa, madatsun ruwa da noman rani a yankin Arewa da sauran sassan Najeriya.

Babachir ya kara da cewa akwai madatsun ruwa da dama a Arewacin Najeriya da ke bukatar gyara da inganta amfani da su, don samar da ruwa da bunkasa noma.

Dangane da Peter Obi, Babachir ya ce ya kamata tsohon gwamnan Anambra ya fi mayar da hankali wajen bayyana manufofinsa ga jama’a a duk lokacin da ya samu damar ganawa da magoya bayansa.

Ya ce ziyartar coci ko halartar taruka ba zai wadatar ba idan ba a yi amfani da irin wadannan damar wajen bayyana shirye-shiryen da za a aiwatar idan aka samu mulki ba.

Babachir ya ba da misali da wasu muhimman batutuwan kasa, ciki har da hako man fetur a Kolmani da samar da wutar lantarki daga aikin Mambilla, yana mai cewa ya kamata ‘yan takarar su bayyana yadda za su magance irin wadannan matsaloli.

A cewarsa, idan Obi da Kwankwaso suka fi mayar da hankali wajen bayyana manufofinsu da yadda za su inganta rayuwar jama’a, hakan na iya taimaka musu wajen samun karin karbuwa a zaben 2027.

Babachir David Lawal, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NDC bayan barin wasu jam’iyyun siyasa, na daga cikin ‘yan siyasar da ke taka rawa wajen tattaunawa kan yadda jam’iyyar za ta kalubalanci jam’iyyar APC a zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments