Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAyyukan 'ceto' na sauya fasalin jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal

Ayyukan ‘ceto’ na sauya fasalin jihar Zamfara – Gwamna Dauda Lawal

Gwamnan ya ce gyare-gyare da ayyukan raya kasa na taimakawa wajen samar da ci gaba mai dorewa a jihar

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatin jihar na aiwatar da ayyuka da sauye-sauye a muhimman fannoni a karkashin abin da ya kira “aikin ceto”, domin sauya jihar da kuma inganta rayuwar al’ummar ta.

Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bukukuwan cika shekaru 30 da kafuwar Jihar Zamfara. An kafa jihar ne a ranar 1 ga Oktoba, 1996, bayan an balle ta daga tsohuwar Jihar Sokoto.

An gudanar da bukukuwan ne tare da bikin ranar samun ’yancin kan Najeriya, inda suka samu halartar Jibril Yakubu, tsohon shugaban mulkin soja na farko na Zamfara; Ahmed Sani Yarima da Mahmud Aliyu Shinkafi, tsoffin gwamnonin jihar, da sauran manyan baki.

Da yake jawabi a faretin bikin ranar ’yancin kan Najeriya da bikin cika shekaru 30 da kafuwar Zamfara a filin Trade Fair Complex da ke Gusau, Gwamnan ya ce jihar ta bar wani yanayi na yanke kauna zuwa zamanin da ake samun aiwatar da ayyuka a fili, gaskiya da kuma ci gaba mai dorewa.

Gwamnan ya bukaci sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ma’aikatan gwamnati, ’yan kasuwa da matasa da su hada kai wajen kare zaman lafiya da bunkasa jihar.

Ya ce: “Dole ne mu ajiye rarrabuwar kawuna — ta kabilanci, siyasa da bangaranci — sannan mu kare zaman lafiyar da muka yi fafutuka aka samu.”

A ranar Juma’a, Lawal ya kaddamar da kashi na uku na gyaran tare da zamanantar da sakatariyar J.B. Yakubu da ke Gusau, babban birnin jihar.

Gwamnan ya ce aikin na daga cikin kokarin sake gina cibiyoyin gwamnati da samar da tsarin aikin gwamnati na zamani, mai inganci kuma wanda ke amfani da fasahar zamani.

Ya bayyana cewa gyaran sakatariyar zai inganta hadin gwiwa tsakanin ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati, tare da karfafa sadarwa da kuma taimakawa wajen aiwatar da shawarwarin gwamnati cikin sauri.

Sakatariyar J.B. Yakubu na dauke da wasu ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati da ke da alhakin tafiyar da harkokin mulki da samar da ayyukan jama’a.

Yakubu, wanda shi ne shugaban mulkin soja na farko a jihar, ya yabawa gwamnatin Lawal, musamman kan ayyukan da ta gudanar a fannonin gine-gine, ilimi da lafiya.

Haka kuma, Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya kaddamar da sabon masallacin Juma’a da aka sake ginawa tare da yi masa kwaskwarima, wanda aka fi sani da Masallacin Yardole, da kuma katafaren rukunin shagunan da ke makwabtaka da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments