Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen waje2039: Musulmai za su yi aikin Hajji 2 a shekara guda

2039: Musulmai za su yi aikin Hajji 2 a shekara guda

Shekarar 2039 na ta Miladiyya na iya zama shekara ta musamman ga Musulmai, inda ake hasashen za a gudanar da bukukuwan Idi uku a cikin shekara guda.

Shekarar 2039 na ta Miladiyya na iya zama shekara ta musamman ga Musulmai, inda ake hasashen za a gudanar da bukukuwan Idi uku a cikin shekara guda.

A cewar kalandar Umm al-Qura, ana sa ran Idin Layya zai kasance ranar 5 ga Janairu, sannan Idin Ƙaramar Sallah ya kasance 19 ga Oktoba, kafin a sake samun Idin Layya a ranar 26 ga Disamba.

Haka kuma, shekarar 2039 za ta ƙunshi manyan ibadun Hajji na shekaru biyu na Hijira, wato 1460 AH da 1461 AH.

Dalilin wannan yanayi shi ne kalandar Musulunci ta wata, wadda shekararta ta fi ta Gregorian gajarta da kusan kwanaki 10 zuwa 11, lamarin da ke sa watannin Hijira su riƙa komawa baya a kalandar Miladiyya.

Sai dai waɗannan ranakun hasashe ne bisa kalandar Umm al-Qura, kuma za su iya sauyawa kafin hukumomi su sanar da ranakun hukuma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments