Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga mabiya ɗariƙar Qadiriyya da sauran al’ummar jihar su ci gaba da bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa goyon baya gabanin zaɓen 2027.
Gwamnan ya yi kiran ne ranar Asabar yayin taron Maukibin Kadiriyya da aka gudanar a Kano, wanda ya samu halartar malaman addini, ’yan siyasa da sauran manyan baki daga sassa daban-daban na ciki da wajen ƙasar.
A cewarsa, taron ya kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da goyon bayan jagorancin Tinubu.
A yayin taron, an ƙaddamar da sabon dandamalin Maukibi da gwamnatin Kano ta gina, inda wakilin Shugaba Tinubu, Ibrahim Kabir Masari, ya jagoranci ƙaddamar da shi.
Taron ya kuma samu halartar tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari, da tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, tare da dubban mabiya ɗariƙar Qadiriyya.