A ranar 3 ga Watan Oktoba, Shekarar 1995, wata kotu a Amurka ta wanke fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Amurka, O.J. Simpson, daga zargin kashe tsohuwar matarsa, Nicole Brown Simpson, da abokinta, Ronald Goldman.
Shari’ar ta jawo hankalin miliyoyin mutane a faɗin duniya, inda kafafen yaɗa labarai suka yi mata laƙabi da “Shari’ar Ƙarni” saboda muhimmancinta da yadda ta ɗauki hankalin jama’a.
Shari’ar ta fara ne bayan an gano gawar Nicole Brown da Ronald Goldman a Los Angeles a watan Yunin 1994. An zargi Simpson da hannu a kisan nasu, lamarin da ya haifar da gagarumar muhawara a Amurka.
A yayin gudanar day shari’ar, lauyoyin ɓangarorin biyu sun gabatar da hujjoji daban-daban, yayin da ake ta muhawara kan ingancin shaidun da ’yan sanda suka tattara.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a shari’ar shi ne safofin hannu da aka gabatar a matsayin shaida. Mai gabatar da ƙara ya yi ƙoƙarin danganta safofin hannun da Simpson, amma lokacin da ya gwada su a kotu, ya bayyana cewa ba su yi masa ba.
Lauyoyinsa sun yi amfani da wannan wajen ƙalubalantar hujjojin masu gabatar da ƙara, duk da cewa wannan ba ita ce hujjar da ta kaɗai ta tabbatar da sakamakon shari’ar ba.
Hukuncin ya haifar da rarrabuwar ra’ayi a tsakanin al’ummar Amurka, musamman dangane da launin fata da yadda ake gudanar da aikin ’yan sanda.
Wasu sun yi maraba da wanke Simpson, yayin da wasu suka nuna rashin gamsuwa da hukuncin. Sai dai a shekarar 1997, wata kotun farar hula ta same shi da alhakin mutuwar Nicole Brown da Ronald Goldman, tare da umartar sa ya biya iyalansu Diyya ta dala miliyan 33.5.
Duk da wanke shi a shari’ar kisan, Simpson ya sake fuskantar wata shari’a ta daban a Las Vegas a shekarar 2008, inda aka same shi da laifin fashi da makami da wasu laifuka.
An yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 33, amma aka sake shi a shekarar 2017 bayan ya yi kusan shekaru tara a gidan yari.
O.J. Simpson ya rasu a ranar 10 ga Afrilu, 2024, yana da shekaru 76, bayan fama da cutar kansa. Shari’arsa ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun shari’o’in da suka yi tasiri a tarihin shari’a da zamantakewar Amurka.