Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta yi gargadi game da kalubalantar dokar hana hawa a...

Gwamnatin Kano ta yi gargadi game da kalubalantar dokar hana hawa a jihar

Gargadin ya biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu na Sarkin Dawaki Babba, inda ya yi magana kan takunkumin da gwamnati ta sanya wa ayyukan hawa

Gwamnatin Kano ta gargadi sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, malaman addini da shugabannin al’umma kan yin kalamai ko ɗaukar matakan da za su iya ƙarfafa mutane su ƙi bin umarnin doka ko barazana ga zaman lafiya a jihar.

Gargadin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara kan shari’a da harkokin kundin tsarin mulki, Aminu Hussaini, ya fitar.

Sanarwar ta biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu na Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’Agundi, inda ya yi magana kan takunkumin da gwamnati ta sanya wa hawa dawakai da kuma yadda yake kallon shari’o’in da ke gudana kan masarautar Kano.

Aminu Hussaini ya ce ‘yan ƙasa na da ’yancin bayyana ra’ayoyinsu kan batutuwan da suka shafi jama’a. Sai dai ya jaddada cewa kotuna ne ke da alhakin fassara, fayyace da kuma tabbatar da aiwatar da umarnin kotu.

Ya ce fassarar da mutum ya yi wa umarnin kotu da kansa ba ta ba shi ikon doka na yin watsi da umarnin da wata hukuma mai iko ta bayar.

A cewarsa, duk wanda yake ganin umarnin gwamnati ya saɓa wa umarnin kotu ya kamata ya garzaya kotu domin neman ƙarin bayani ko amfani da sauran hanyoyin da doka ta tanada.

Ya kuma buƙaci irin waɗannan mutane da kada su bayyana aniyarsu ta bijire wa umarnin ko su ƙarfafa wasu su yi hakan.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin masarautar Kano da su bar kotuna su kammala shari’o’in da ke gabansu ba tare da ɗaukar cewa sun san hukuncin da za a yanke ba.

Ta gargadi sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, malaman addini da shugabannin al’umma, da kuma sauran jama’a da su guji kalamai ko ayyukan da ka iya haifar da bijire wa doka, arangama ko kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.

Ofishin mai ba gwamnan shawara ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin jihar na bin doka, kare ’yancin da kundin tsarin mulki ya tanada, tabbatar da ’yancin kotuna da kuma warware rikice-rikice cikin lumana.

Gwamnatin ta kuma yi gargadin cewa ba za ta bari wani mutum ko wata ƙungiya ta yi amfani da rikicin da ake ciki wajen kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa duk wani yunƙuri na tara mutane domin bijire wa umarnin doka, hana hukumomi gudanar da aikinsu ko tayar da tarzoma, za a ɗauki matakin gaggawa a kansa bisa tanadin doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments