Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn yi garkuwa da mata manoma 47 a Jihar Neja

An yi garkuwa da mata manoma 47 a Jihar Neja

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da sace wasu mata manoma da ke aiki a gonar gyaɗa a ƙauyen Mukura, gundumar Kasuwan-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga.

Mai magana da yawun rundunar, Sufeto Wasi’u Abiodun, ya ce an samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da fiye da mutane 20 a yankin ranar 27 ga Satumba da misalin ƙarfe 3 na rana.

Sai dai Shugaban Ƙaramar Hukumar Mariga, Aliyu Muhammadu, ya ce adadin mutanen da aka sace ya kai 47, kuma dukkansu mata ne da ke aikin gona. Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin matan ta haihu ne yayin da take hannun masu garkuwar.

A cewar shugaban ƙaramar hukumar, masu garkuwar sun tuntubi iyalan waɗanda aka sace, inda suka buƙaci Naira miliyan biyu kan kowacce mace a matsayin kuɗin fansa.

Rundunar ’yan sanda ta ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa suna ci gaba da ƙoƙarin gano inda waɗanda aka sace suke tare da ceto su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments