Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana goyon bayansa ga ƙungiyar Tinubu Must Go (TMG), wadda ke kira da a kawo sauyi a mulkin Najeriya.
Atiku ya bayyana hakan ne bayan ya karɓi Abba Hikima Esq., ɗaya daga cikin manyan jagororin sauyin TMG na ƙasa baki ɗaya.
Ya ce ƙungiyar ta gudanar da ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a a faɗin Najeriya, inda mutane 109,799 suka shiga.
“Na ji daɗin yadda jama’a suka nuna sha’awarsu da shiga cikin wannan ƙuri’a, inda takarata ta samu gagarumin rinjaye da kashi 73.6 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.”
Atiku ya ce abin da ya fi muhimmanci ba sakamakon ƙuri’ar kaɗai ba ne, sai dai irin fatan da take wakilta na neman sauyi a ƙasar.
“Abin da ya fi muhimmanci fiye da sakamakon ƙuri’ar shi ne babban fatan da take wakilta: ƙarin buƙatar sauyi da ’yan Najeriya ke nunawa a matakin ƙasa, da kuma ƙudurin haɗin kan jama’a na ceto Najeriya daga halin da take ciki.”
Ya ce ya amince da ƙungiyar, tare da kira ga ’yan Najeriya masu ra’ayin sauyi da su shiga cikinta domin cimma wannan manufa.