Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSanata Barau ya kori Rashida Mai Sa’a daga mukamin maitaimakiyarsa

Sanata Barau ya kori Rashida Mai Sa’a daga mukamin maitaimakiyarsa

An zarge ta da yin kalamansiyasa da suke bata sunan APC da cin fuska ga Sanata Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kori Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a, daga mukaminta na mai ba shi shawara ta musamman.

An ce matakin ya biyo bayan wasu kalaman da Rashida ta yi, wadanda ofishin Sanata Barau ya bayyana cewa sun shafi siyasar jam’iyya da kuma bata sunan jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Sanarwar korar na kunshe a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun Sanata Barau, Shitu Madaki Kunchi, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce an cire Rashida daga mukaminta ne saboda wasu kalaman da aka bayyana a matsayin masu tunzura magoya baya da kuma yin siyasar jam’iyya.

Ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya ce irin wadannan kalamai ba su dace da matsayinta na ma’aikaciya a ofishin ba.

Sanarwar ta kuma zargi Rashida da yin wasu kalamai da aka danganta da “Anti-Party”, wato aiki ko magana da za ta iya sabawa muradun jam’iyyar, tare da cin fuska ga Sanata Barau.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments