Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ɗan takararta na shugaban ƙasa, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, zai samar da gwamnati mai sauraron jama’a da kuma amsa bukatunsu idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.
Kwamitin ya ce Atiku ba zai zama “shugaban ƙasa wanda ba ya nan” ba, yana mai cewa zai kasance a shirye domin tunkarar manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Majalisar Yaƙin neman zaɓen ADC, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja yayin da yake karɓar shugabannin Atiku Unity Movement (AUM), ƙarƙashin jagorancin Hon. Francis Eburuwe.
Ologbondiyan ya ce Atiku ya fahimci matsalolin tattalin arziki da zamantakewar Najeriya, tare da gabatar da manufofin da za su taimaka wajen magance su.
Ya tuna cewa a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya goyi bayan cire tallafin man fetur a hankali, yana mai cewa bai kamata tsarin ya jefa ’yan Najeriya cikin tsananin matsin j89rayuwa ba.
A cewarsa, abubuwan da suka faru cikin shekaru uku da suka gabata sun ƙara nuna muhimmancin samun shugaban ƙasa mai kusanci da jama’a, mai saurin amsa koke kuma mai iya ɗaukar matakan da suka dace cikin lokaci.
“Ƙasar na buƙatar shugaban ƙasa wanda ya fahimci ƙalubalen da ’yan Najeriya ke fuskanta, kuma yake nan da kansa domin mayar da martani ga buƙatun shugabanci.
“Ba za a iya barin Najeriya cikin yanayin da ake shakku kan wanda ke jagorantar al’amuran gwamnati yadda ya kamata a lokuta masu muhimmanci ba. Ƙasar na buƙatar shugabanci mai ƙarfi da mai da hankali,” in ji shi.
Ologbondiyan ya ƙara da cewa tsarin mulkin Atiku zai mayar da hankali kan magance matsalolin tattalin arziki, inganta jin daɗin ’yan ƙasa da kuma dawo da amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati.
Ya kuma ce wasu daga cikin sabbin manufofin tattalin arzikin da Atiku ya gabatar sun mayar da hankali kan rage wa jama’a nauyin hauhawar farashin makamashi da tsadar rayuwa.
Atiku ya gabatar da shawarar samar da wani tsari na tallafawa man fetur da aka tace a cikin Najeriya, tare da sanya iyakar kuɗin da za a kashe, samun amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa kan yadda aka kashe kuɗin.
Tun da farko, shugaban tawagar Atiku Unity Movement, Hon. Francis Eburuwe, ya ce ƙungiyar na nan daram kan goyon bayan takarar Atiku, kuma za ta ƙara himma wajen wayar da kan ’yan Najeriya kan abin da ya bayyana a matsayin buƙatar sauya salon tafiyar da siyasar ƙasar.
Eburuwe ya ce ƙungiyar za ta kai saƙon takarar Atiku ga ’yan Najeriya a sassa daban-daban na ƙasar, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnatin Atiku za ta magance matsalolin ƙasar tare da inganta rayuwar jama’a.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da bai wa yaƙin neman zaɓen ADC goyon baya, tare da kira ga mambobin ƙungiyar da su ci gaba da ƙarfafa ayyukan wayar da kai a matakin ƙasa da ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.