Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNajeriya na neman sabon rancen Dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya

Najeriya na neman sabon rancen Dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya

Najeriya na neman sabon rancen kuɗi da ya kai Dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya domin tallafa wa wasu shirye-shiryen gwamnati da suka shafi yaƙi da sauyin yanayi, kare al’umma da bunƙasa yara a shekarunsu na farko.

Bayanan gwamnati sun nuna cewa za a yi amfani da kuɗin wajen aiwatar da matakan da za su taimaka wajen rage illolin sauyin yanayi, ƙarfafa shirye-shiryen kare al’umma da kuma inganta rayuwar yara ƙanana.

Sabon bashin na zuwa ne yayin da jimillar bashin gwamnatin Najeriya ke ƙaruwa.

Bayanai sun nuna cewa bashin gwamnati ya kai naira tiriliyan 166.8, kwatankwacin Dala biliyan 125.6, a watan Yunin 2026.

Idan aka amince da sabon rancen, zai ƙara cikin bashin da gwamnatin Najeriya ke bi, yayin da hukumomi ke ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da aka ce za a yi amfani da kuɗin wajen tallafa musu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments