Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaYan garin Atiku ma APC suka zaba a zaben cike gurbi -...

Yan garin Atiku ma APC suka zaba a zaben cike gurbi – Yilwatda

Shugaban APC na ƙasa ya ce jam’iyyun ADC da NDC ba za su zama babban ƙalubale ga jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi watsi da barazanar da jam’iyyun adawa ke yi gabanin babban zaɓen 2027.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taron kwanaki uku na jam’iyyar da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Taron ya samu halartar mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC), wasu zaɓaɓɓun mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), da shugabannin APC na jihohi.

Shugaban APC ya ce sakamakon zaɓukan cike gurbi guda biyar da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar ya nuna cewa jam’iyyar na da ƙarfin da za ta iya lashe zaɓen 2027.

Ya ce APC ta samu nasara a huɗu daga cikin zaɓukan, yayin da ta sha kaye a zaɓe guda ɗaya a hannun APM, ba wai manyan jam’iyyun adawa da ake yawan magana a kansu ba.

Ya ce, “Mun je Ekiti kuma muka zo na ɗaya; jam’iyyar da ta zo ta biyu ita ce PDP, ba wai waɗannan jam’iyyun adawa da ake kira ADC da NDC ba. Mun je Osun kuma muka zo na biyu, babu ɗaya daga cikin waɗannan jam’iyyun siyasa da kuka ce sun yi nasara da ya taɓa lashe ko kujerar kansila.”

Yilwatda ya ƙara da cewa, “Idan har ba za su iya lashe kujerar kansila ba, shin da gaske muna fafatawa da su ne? A ganina, su masu halartar wannan zaɓe ne kawai, ba masu fafatawa da mu ba. Muna da cikakken yaƙinin cewa jam’iyyarmu za ta iya lashe wannan zaɓe, kuma mun shirya tsaf domin lashe zaɓen 2027.”

Ya kuma ambaci wasu zaɓuka da aka gudanar a Osun da kuma zaɓukan majalisu a jihohin Arewa da suka haɗa da Kano, Bauchi da Gombe, inda ya ce APC ta nuna ƙarfi.

Shugaban jam’iyyar ya ce abubuwan da ake yadawa a kafafen yaɗa labarai game da ƙarfin jam’iyyun adawa ba su yi daidai da abin da ke faruwa a zahiri ba.

Ya ce, “Ko a makon da ya gabata, mun yi zaɓen cike gurbi a Adamawa, a ƙaramar hukumar Ganye, inda Atiku ya fito, kuma mun lashe zaɓen. Muna da ƙarfi sosai a ƙasa, kuma ina shakkun ko akwai wata jam’iyya da za ta iya ƙalubalantar mu.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments