Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNeja: Gwamnati ta ba kwamitin binciken mutuwar mahakan ma'adanai wa'adin mako 2

Neja: Gwamnati ta ba kwamitin binciken mutuwar mahakan ma’adanai wa’adin mako 2

Harkokin Cikin Gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bai wa kwamitin mutum 10 mai zaman kansa wa’adin makonni biyu domin kammala bincike kan mutuwar mutane 37 a jihar Neja, lamarin da ya shafi jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC).

A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, ministan ya bukaci kwamitin ya gudanar da binciken cikin ’yanci ba tare da tsoma bakin kowa ba, domin tabbatar da adalci ga mamatan da iyalansu.

Kwamitin zai binciki ainihin adadin mutanen da suka mutu da kuma musabbabin mutuwarsu, ta hanyar amfani da hanyoyin binciken kimiyya.

Haka kuma, zai duba ko an samu sakaci, aikata ba daidai ba, haɗin baki ko kuma keta doka a yayin faruwar lamarin.

Gwamnatin ta kuma bukaci kwamitin ya ba da shawarwari kan matakan da suka dace, ciki har da hukuncin da ya kamata a ɗauka da kuma diyyar da ya kamata a bai wa iyalan waɗanda suka mutu.

Za a kuma nemi shawarwari kan hanyoyin da za su taimaka wajen hana sake faruwar irin wannan lamari.

Tunji-Ojo ya umarci shugabannin NSCDC da jami’an da lamarin ya shafa su ba kwamitin cikakken haɗin kai tare da kare dukkan bayanai da hujjojin da suka shafi binciken.

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin lalata ko ɓoye hujja, tsoratar da shaidu ko kawo cikas ga binciken za a ɗauke shi a matsayin babban laifi.

Kwamitin, wanda Jonathan Kure ke jagoranta, ana sa ran zai fara aiki nan take tare da miƙa rahotonsa cikin wa’adin makonni biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments