Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroJami’an tsaro sun hallaka yan bindiga 18 a Jihar Katsina

Jami’an tsaro sun hallaka yan bindiga 18 a Jihar Katsina

Rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro ta kashe mutane 18 da ake zargi da kasancewa ’yan bindiga a wani samame da ta gudanar a Ƙaramar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Nasir Mu’azu, ya fitar.

A cewar sanarwar, an gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar 21 ga Satumba a ƙauyen Gidan Iyado da ke yankin Kakumi, bayan jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kan shirin wasu ’yan bindiga na kai hari da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Mafarauta, dakarun CWC da ’yan sa-kai ne suka haɗa kai wajen gudanar da aikin, inda suka yi wa ’yan bindigar kwanton bauna.

A yayin arangamar, an kashe 18 daga cikin waɗanda ake zargin ’yan bindiga ne.

Jami’an tsaron sun kuma kwato bindigar G3 guda ɗaya, AK-47 guda biyu, harsasai 14, babura uku, shanu biyu da tumaki 94 da ake zargin an sace.

Ma’aikatar ta ce babu jami’in tsaro da ya rasa ransa ko ya samu rauni yayin arangamar.

Haka kuma, an ce ana ci gaba da farautar shugaban ƙungiyar da ake zargi, wanda ya tsere yayin musayar wuta.

Kwamishinan ya yaba da haɗin gwiwar mafarauta, dakarun CWC da ’yan banga, tare da kira ga mazauna jihar da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments