Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin sakin fasfon tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha na Najeriya, Uche Nnaji, domin ya samu damar tafiya ƙasar waje don duba lafiyarsa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta amince da buƙatar da lauyan Nnaji, Cif Ogwu Onoja, SAN, ya gabatar a ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ministan ya nemi izinin tafiya ƙasashen waje ne domin ganin likita, inda kotun ta amince a mayar masa da fasfon nasa na ɗan lokaci domin gudanar da tafiyar.
Nnaji dai na fuskantar tuhuma daga Hukumar ICPC kan laifuffuka shida da suka haɗa da zargin amfani da takardun bogi, bayar da bayanan ƙarya da rashin gaskiya a aiki.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa tsohon ministan ya karɓi naira miliyan 29.5 a matsayin albashi da alawus-alawus ba bisa ƙa’ida ba a lokacin da yake riƙe da muƙaminsa.
A baya, kotun ta bayar da belinsa kan kuɗi naira miliyan 20, tare da sharadin ajiye fasfonsa a kotu da kuma samar da wanda zai tsaya masa.
A halin yanzu, an ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga Oktoba, 2026.
Rahoton ya ce ba a bayyana sunan ƙasar ko asibitin da Nnaji zai je domin duba lafiyarsa ba.