Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Zamfara ya ƙara albashin ma’aikatan lafiya da 95%

Gwamnan Zamfara ya ƙara albashin ma’aikatan lafiya da 95%

Kwamishinar lafiya ta ce ƙarin albashin zai inganta walwala da ƙwazon ma’aikatan lafiya.

Kwamishinar Lafiya ta Jihar Zamfara, Dr. Nafisa Muhammad Maradun, ta yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa amincewa da ƙarin albashin ma’aikatan lafiya a jihar da kashi 95 cikin 100.

Dr. Maradun ta bayyana hakan ne a ranar Litinin a ofishinta, yayin da take magana game da sabon tsarin da gwamnati ta dauka na amincewa da sabon tsarin albashin ma’aikatan lafiya.

Ta ce matakin wani muhimmin yunkuri ne na inganta walwala da kuma yanayin aikin ma’aikatan lafiya a jihar.

Sabon tsarin albashin ya dogara ne kan tsarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi ga ma’aikatan lafiya, musamman CONHESS.

A cewar kwamishinar, sake duba albashin na daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ke aiwatarwa domin farfaɗo da fannin lafiya da kuma inganta walwala da yanayin aikin ma’aikatan lafiya.

Dr. Maradun ta ce ƙarin albashin ya ƙara nuna ƙudurin gwamnatin jihar na ƙarfafa fannin lafiya da tallafa wa ma’aikatan lafiya domin su samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar Zamfara.

Ta yi kira ga ma’aikatan lafiya a faɗin jihar da su mayar da martani ga wannan kyakkyawan mataki na gwamnati ta hanyar ƙara jajircewa wajen gudanar da ayyukansu tare da mara wa ƙoƙarin gwamnati na inganta harkokin kiwon lafiya baya.

Kwamishinar ta kuma yi gargaɗin cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da rashin zuwa aiki ko sakaci da aiki daga wasu ma’aikatan lafiya ba.

Ta bukace su da su nuna ƙwarewa, jajircewa da sadaukarwa wajen sauke nauyin da ke kansu.

Dr. Maradun ta gode wa Gwamna Lawal bisa bai wa walwalar ma’aikatan lafiya muhimmanci da kuma ɗaukar matakan ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments