Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa2027: Yari ya jagoranci tawagar APC wajen neman goyon bayan manyan malamai

2027: Yari ya jagoranci tawagar APC wajen neman goyon bayan manyan malamai

Tuni wasu daga cikin malaman suka ayyana goyon baya ga tazarcen Bola Ahmed Tinubu

Sanata Abdulaziz Yari ya jagoranci tawagar jam’iyyar APC zuwa jihohin Arewa domin neman goyon bayan manyan malaman Musulunci ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Tawagar, wadda ta ƙunshi manyan jami’an APC, ta ziyarci jihohin Plateau, Bauchi, Kaduna da Kano, inda ta gudanar da tarukan sirri da fitattun malaman addinin Musulunci daga ƙungiyoyin Izala, Tijjaniyya, JIBWIS da Ƙadiriyya.

Daga cikin waɗanda suka raka tsohon Gwamnan Jihar Zamfara akwai Shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje; tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Adamu Aliero; tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff; da Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Sanata Nasiru Sani Zangon Daura, tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Ahmed Idris Wase, da Hon. James Abiodun Faleke.

Tawagar ta fara shawarwarin ne a Jos, Jihar Plateau, inda Sheikh Sani Yahaya Jingir, Shugaban Majalisar Ulama ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), ya tarbe su.

Daga nan tawagar ta je Jihar Bauchi, inda ta gana da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, Khalifan Zawiyyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Malamin ya yi addu’a ga Shugaba Tinubu tare da kira ga gwamnati da ta ci gaba da tattaunawa da al’ummomin addini a duk shekara, maimakon jiran lokacin zaɓe kawai.

A Kaduna, Sanata Yari ya gudanar da tattaunawa mai zurfi da Sheikh Abdullahi Bala Lau, Shugaban JIBWIS na ƙasa, reshen Kaduna.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan muhimman batutuwan ƙasa da suka haɗa da tsaro a yankuna daban-daban, matsin tattalin arziki da ake fuskanta, da hanyoyin sake gina amana tsakanin al’ummomin ƙabilu daban-daban.

Sheikh Bala Lau ya yabawa matakin tuntubar malaman, amma ya yi kira ga shugabannin siyasa a dukkan matakai da su riƙa sadarwa da jama’a cikin gaskiya tare da mai da hankali kan matsalolin talakawa.

An kammala rangadin tuntubar malaman ne a Kano, inda tawagar ta ziyarci shugaban Ƙadiriyya, Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments