Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage zaman kotu zuwa 26 ga Oktoba, 2026, domin yanke hukunci kan buƙatar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na cewa ba wata shari’a da ya kamata a yi da shi game da zargin kutse a wayar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ta ƙasa, Nuhu Ribadu.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ce ta shigar da ƙarar da ake zargin El-Rufai da kutse ko sauraron sadarwar wayar Ribadu, tare da zargin karya dokokin tsaron ƙasa.
El-Rufai, wanda ya kasance gwamnan Kaduna daga 2015 zuwa 2023, ya musanta zarge-zargen, inda ya ce ba shi da laifi.
A zaman kotun, lauyan El-Rufai, Paul Erokoro (SAN), ya roƙi kotun ta amince da buƙatar neman a sallame shi, yana mai cewa masu gabatar da ƙara sun gaza gabatar da hujjojin da suka isa su tabbatar da cewa akwai shari’ar da za ta tilasta wa wanda yake karewa ya shiga matakin kare kansa.
A nasa martanin, lauyan DSS, Oluwole Aladedoye (SAN), ya dogara da martanin da hukumar ta gabatar kan buƙatar, inda ya roƙi kotun ta yi watsi da ita tare da umartar El-Rufai ya fara kare kansa.
Aladedoye ya ce lauyoyin El-Rufai ba su yi cikakken bayani kan hujja ta B ba, wadda masu gabatar da ƙara suka ce tana ɗauke da abin da suke ganin ikirari ne daga El-Rufai game da sauraron sadarwar wayar Ribadu.
Bayan sauraron bangarorin biyu, Mai shari’a Abdulmalik ta ɗage shari’ar zuwa 26 ga Oktoba domin yanke hukunci kan buƙatar.
A baya DSS ta gabatar da shaidu biyu, ciki har da wani jami’in hukumar da kuma lauya mai kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju.
Sun yi wa kotu bayani kan kalaman da ake zargin El-Rufai ya yi a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin game da sauraron sadarwar da ta shafi mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu.
A yayin shari’ar, kotun ta kalli faifan hirar da aka yi da El-Rufai, inda ake zargin ya ce: “Mun saurari tattaunawar NSA.”
Adeyanju ya shaida wa kotun cewa bai ji El-Rufai ya fito fili ya ce ya kutsa cikin wayar Ribadu ba, amma ya ji shi yana cewa sun saurari tattaunawar NSA.
El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhume guda biyar da aka yi wa kwaskwarima, da suka shafi zargin kutse a sadarwar wayar Ribadu da kuma karya dokokin tsaron ƙasa.