Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta yi nasarar dawo da ‘yan Najeriya 50,000 daga ƙasashen...

Gwamnatin tarayya ta yi nasarar dawo da ‘yan Najeriya 50,000 daga ƙasashen waje

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Baƙin Haure da Masu Gudun Hijira a Cikin Gida (NCFRMI) ta ce ta taimaka wajen dawo da ‘yan Najeriya kimanin 50,000 da suka kasance ‘yan gudun hijira a ƙasashen waje cikin shekaru uku

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Baƙin Haure da Masu Gudun Hijira a Cikin Gida (NCFRMI) ta ce ta taimaka wajen dawo da ‘yan Najeriya kimanin 50,000 da suka kasance ‘yan gudun hijira a ƙasashen waje cikin shekaru uku.

Kwamishinan hukumar, Aliyu Ahmed, ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin cika shekaru uku da ya yi a matsayin shugaban hukumar.

Ya ce hukumar na kula da sama da mutane miliyan 6.7 da suka rasa matsugunansu a Najeriya, ciki har da waɗanda ke zaune a sansanoni da kuma cikin al’ummomin da suka karɓe su.

Ahmed ya ce Najeriya na kuma karɓar ‘yan gudun hijira daga wasu ƙasashe, yayin da wasu ‘yan Najeriya ke zaune a matsayin ‘yan gudun hijira a ƙasashe kamar Kamaru, Nijar, Chadi da Laberiya.

Ya ƙara da cewa kwanan nan Najeriya ta karɓi ‘yan ƙasa 1,400 daga Afirka ta Kudu, yana mai cewa hukumar na ƙoƙarin samar da ingantattun bayanai kan ‘yan gudun hijira da sauran mutanen da suka rasa matsugunansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments