Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya yi cikakken bayani kan tushen doka da kuma yadda za a samar da kuɗaɗen shirin tallafin fetur da ya gabatar domin rage farashin man fetur a Najeriya.
Kwamitin, ta bakin mai magana da yawunsa, Dele Alake, ya ce shirin tallafin fetur ɗin da ake tacewa a cikin gida ya haifar da tambayoyi kan yadda za a aiwatar da shi bisa doka, da kuma ko za a wajabta wa matatun mai da za su amfana da tallafin sayar da fetur a farashin da gwamnati ta kayyade.
APC ta kuma nemi Atiku ya bayyana adadin kuɗin da shirin zai lakume, inda za a samo su, yawan man da za a tallafa wa da kuma matakan da za a ɗauka domin hana karkatar da fetur da fasa-ƙaurinsa.
Kwamitin ya yi iƙirarin cewa shirin na iya lakume tsakanin Naira tiriliyan 17 zuwa tiriliyan 21 a shekara, yana mai buƙatar a fayyace yadda tsarin zai bambanta da tsohon tsarin tallafin fetur da kuma yadda zai dace da dokokin man fetur na ƙasar.
A nasa ɓangaren, kwamitin ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na mayar da hankali wajen bunƙasa amfani da CNG da motocin lantarki a matsayin wasu hanyoyin rage kuɗin sufuri da nauyin tsadar makamashi ga ‘yan Najeriya.