Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaShettima: Gwamnonin Arewa shida ne kawai suka goyi bayan Tinubu a 2023

Shettima: Gwamnonin Arewa shida ne kawai suka goyi bayan Tinubu a 2023

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnonin jihohin Arewa shida ne kawai cikin 19 suka goyi bayan takarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a fadar Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, yayin bikin naɗa Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, sarautar Sardaunan Masarautar Ilorin.

Sai dai mataimakin shugaban ƙasar bai bayyana sunayen gwamnonin da ya ce sun goyi bayan Tinubu a lokacin zaɓen ba.

A zaɓen na 2023, Tinubu, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 8,794,726.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya zo na biyu da kuri’u 6,984,520, yayin da Peter Obi na LP ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.

Kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, APC ce ke mulkin jihohi 14 daga cikin 19 na Arewa, yayin da PDP ke mulkin sauran jihohi biyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments