Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeMutane sama da 100,000 a Japan sun kai shekaru 100

Mutane sama da 100,000 a Japan sun kai shekaru 100

Adadin mutanen da suka kai shekaru 100 ko fiye da haihuwa a Japan ya haura 100,000 a karon farko a tarihin ƙasar.

Adadin mutanen da suka kai shekaru 100 ko fiye da haihuwa a Japan ya haura 100,000 a karon farko a tarihin ƙasar.

Ma’aikatar Lafiya ta Japan ta ce sabbin ƙididdiga sun nuna cewa akwai akalla mutane 107,677 da suka kai wannan shekaru, inda mata ke da kaso mafi yawa, wato kashi 88 cikin 100 na adadin.

A halin yanzu, Kishimoto Fuyo, mai shekaru 114 daga Kyoto, ita ce mace mafi tsufa a ƙasar, yayin da Kato Hikaru, mai shekaru 112 daga Kumamoto, shi ne namijin da ya fi kowa tsufa.

Ministan Lafiyar Japan, Kenichiro Ueno, ya bayyana farin cikinsa kan yadda mutane ke samun damar rayuwa tsawon lokaci cikin koshin lafiya. Ya ce wannan na iya samar da muhimman bayanai ga masu bincike a fannonin kimiyya da fasaha.

Sai dai karuwar yawan tsofaffin mutane na zuwa ne a daidai lokacin da Japan ke fuskantar ƙarancin matasa masu aikin yi, lamarin da ke ƙara jefa ƙasar cikin matsalar ƙarancin ma’aikata.

Masana sun danganta tsawon rayuwar al’ummar Japan da wasu halaye na rayuwa, ciki har da cin abinci mai gina jiki, musamman kifi, shinkafa da kayan lambu, tare da motsa jiki akai-akai.

A gefe guda, yawan tsofaffin mutane ya kuma haifar da ƙarin buƙatar kayayyakin kula da tsofaffi, ciki har da manyan pampers da ake amfani da su wajen taimaka musu wajen kula da bukatunsu na yau da kullum.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments