Rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Tsaron Zaɓe (ICCES) sun kammala shirye-shiryen tsaro domin zaɓen ɗan majalisar jihar mai wakiltar ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da za a gudanar ranar Asabar.
An cimma matsayar ne a wani taron tsaro na musamman da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranta gabanin zaɓen da aka sanya ranar 19 ga Satumba, 2026.
A yayin taron, kwamitin ya duba shirye-shiryen tsaro da rahotannin leƙen asiri, tare da gano wuraren da ka iya zama cibiyar rikici da kuma tantance kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari.
CP Bakori ya ce an tura isassun jami’an tsaro, kayan leƙen asiri da sauran kayan aiki zuwa rumfunan zaɓe, cibiyoyin tattara sakamako da wasu muhimman wurare a faɗin yankin da za a gudanar da zaɓen.
Ya tabbatar wa masu zaɓe, jami’an Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), masu sa ido kan zaɓe da sauran masu ruwa da tsaki cewa za a samar da cikakken tsaro kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.
Kwamishinan ya ce ’yan sanda za su yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro domin kare tsarin zaɓe da tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana da sahihanci.
A nasa bangaren, Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano kuma shugaban ICCES, Ambasada Zango Abdu, ya ce INEC ma ta kammala shirye-shiryenta na zaɓen, ciki har da rarraba kayan zaɓe masu muhimmanci da waɗanda ba su da muhimmanci.
Kwamitin ya kuma yanke shawarar ƙara yawan sintiri na haɗin gwiwa, ƙarfafa hanyoyin gaggauta kai ɗauki da kuma sanya ido kan shafukan sada zumunta domin dakile yaɗa bayanan ƙarya da ka iya haifar da tashin hankali a lokacin zaɓen.
Haka kuma, kwamitin ya yi alƙawarin tabbatar da bin dokokin zaɓe tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu yana karya doka.
’Yan sanda sun buƙaci jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su guji tashin hankali, sayen ƙuri’u da sauran abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaɓen.
Haka kuma, an shawarci mazauna Dawakin Kudu da su kasance masu bin doka tare da sanar da hukumomin tsaro cikin gaggawa idan suka lura da wani mutum ko wani abu da ake zargi.