Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ya yi murabus

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ya yi murabus

Ana zargin Saidu Yahaya ya ajiye muƙaminsa ne bayan matsin lamba daga gwamnatin jihar.

Shugaban Hukumar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Saidu Yahaya, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Majiyar SolaceBase ta ce Yahaya ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne a ranar Talata.

Murabus ɗin nasa ya biyo bayan matsin lamba daga gwamnatin Jihar Kano kan zargin cewa ya gaza sauke nauyin da ake sa ran zai yi a matsayin shugaban hukumar.

An naɗa Yahaya a matsayin shugaban PCACC a watan Agustan 2025, bayan kammala wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ce ta amince da naɗinsa na tsawon shekaru biyar.

A baya-bayan nan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito fili ya soki shugaban hukumar, inda ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda yake gudanar da ayyukansa a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci.

Ana sa ran Sakatariyar Shari’a ta hukumar, Hafsat Kutama, za ta fara aiki a matsayin mukaddashiyar shugabar hukumar daga yau, Laraba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments