Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn sake zargin Malam Lawan Triumph da taɓa janibin Fiyayyen Halitta

An sake zargin Malam Lawan Triumph da taɓa janibin Fiyayyen Halitta

Ƙungiyoyin Musulunci sun kai Malam Lawan Triumph kotu kan wasu kalamansa

Gamayyar wasu ƙungiyoyin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sheikh Albukhari Mikha’il sun kai ƙara Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu, kan Malam Lawan Shu’aibu Triumph.

Ƙungiyoyin sun zargi Malam Lawan Triumph da yin wasu kalamai da suka ce sun kasance ɓatanci ga Janabin Manzon Allah (SAW).

Haka kuma, ƙarar ta ƙunshi zargin cewa Malam Lawan Triumph ya yi wasu kalamai game da Musulman da ke zuwa Saudiyya domin gudanar da ibadar Umarah, musamman waɗanda ke zuwa a lokacin bikin Mauludi.

An shigar da ƙarar ne a gaban kotun da Mai Shari’a Mallam Ibrahim Sarki Yola ke jagoranta.

Bayan karɓar ƙarar, kotun ta sanya gobe Alhamis domin fara sauraron shari’ar.

Ana sa ran kotun za ta fara duba ƙorafe-ƙorafen da ƙungiyoyin suka gabatar, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin ci gaba da shari’ar.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Malam Lawan Shu’aibu Triumph bai mayar da martani kan zarge-zargen da aka gabatar a kansa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments