Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin a tabbatar da sakin dukkan kuɗaɗen da aka amince da su domin hukumomin raya yankuna daban-daban a faɗin ƙasar.
Tinubu ya umarci Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) da ya ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da cewa hukumomin sun karɓi kuɗaɗen da aka ware musu.
Rahotanni sun nuna cewa an ɗauki wannan matakin ne domin bai wa hukumomin damar gudanar da ayyukan raya yankuna da kuma aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da aka ɗora musu.
Ana sa ran sakin kuɗaɗen zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan hukumomin raya yankuna, tare da ba su damar gudanar da ayyukan more rayuwa da sauran shirye-shiryen da za su amfani al’ummomin yankunansu.
Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara kira ga hukumomin raya yankuna su taka rawar gani wajen haɓaka ci gaba da magance wasu daga cikin ƙalubalen da al’ummomi ke fuskanta a sassa daban-daban na Najeriya.