Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciDangote ya ƙaddamar da sayar da hannayen jari biliyan 4.1 na matatar...

Dangote ya ƙaddamar da sayar da hannayen jari biliyan 4.1 na matatar man fetur

Hamshaƙin attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya ƙaddamar da sayar da wasu hannayen jari na matatar man fetur ɗinsa da ke birnin Legas.

Rahotanni sun nuna cewa kamfanin zai sayar da hannayen jari biliyan 4.1 da nufin tara kuɗaɗen da suka kai naira tiriliyan 2.15, kwatankwacin dala biliyan 1.6.

Ana sa ran wannan ciniki zai kasance ɗaya daga cikin mafi girman sayar da hannayen jari a karon farko da aka taɓa gudanarwa a nahiyar Afirka.

Kamfanin ya bai wa masu zuba jari damar neman sayen hannun jarin har zuwa ranar 13 ga watan Oktoba, 2026, lokacin da za a rufe karɓar buƙatun masu sha’awar shiga cinikin.

Bayan kammala karɓar buƙatun, ana sa ran za a fara cinikin hannayen jarin a kasuwa a ƙarshen watan Nuwamba.

A cewar bayanan kamfanin, za a sayar da kowane hannun jari kan kuɗin naira 525.

Wannan ya nuna cewa ƙimar matatar Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals za ta kai kusan naira tiriliyan 63, wanda ya yi daidai da kusan dala biliyan 47.59.

Matakin na zuwa ne yayin da matatar Dangote ke ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkar tace mai a Najeriya da nahiyar Afirka, tare da ƙoƙarin ƙara samar da man fetur da sauran kayayyakin man fetur a cikin gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments