Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan manufofin da gwamnatinsa ta aiwatar, musamman cire tallafin man fetur da kuma sauya tsarin tafiyar da kuɗaɗen waje.
Dangote ya bayyana yabon nasa ne ranar Litinin a Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya da ke birnin Legas, yayin wani taron ƙaddamar da sayar da hannayen jarin kamfanin matatar man fetur ta Dangote ga jama’a.
Hamshaƙin attajirin ya ce kamfaninsa zai ci gaba da aiki tare da gwamnatin tarayya domin ba da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.
Ya kuma nuna mamakinsa kan yadda Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya ta samu gagarumin ci gaba, yana mai cewa bai yi tsammanin kasuwar za ta kai matsayin da take a shekarar 2026 ba.
A yayin taron, kamfanin Dangote ya fara sayar da sabbin hannayen jari biliyan 4.1 na matatar man fetur, inda aka sanya farashin kowanne hannun jari kan naira 525.
Kamfanin ya bayyana cewa mafi ƙarancin hannayen jarin da mutum zai iya saya su ne guda 10, wanda darajarsu ta kai naira 5,250.
Ana sa ran rufe karɓar buƙatun sayen hannayen jarin a ranar 13 ga watan Oktoban shekarar 2026, bisa ga ƙa’idoji da sharuddan da aka tanada domin gudanar da cinikin.