Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBabu tarbiyyar musulunci a wa’azin Albany da dutsen tanshi – Sheikh Gumi

Babu tarbiyyar musulunci a wa’azin Albany da dutsen tanshi – Sheikh Gumi

Wata magana da ake dangantawa da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi, ta bazu a kafafen sada zumunta, inda ake zargin ya bayyana rashin gamsuwarsa da irin wa’azin marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani Zaria da Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi.

A cewar kalaman da ke yawo, an danganta wa Sheikh Gumi cewa bai gamsu da salon wa’azin malaman biyu ba, yana mai cewa bai ga wa’azinsu ya cika wasu fannoni na tarbiyyar Musulunci yadda ya kamata ba.

Sai dai bincike ya nuna cewa har yanzu ba a samu cikakken faifan bidiyo ko wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da lokacin da Sheikh Gumi ya yi wannan magana da kuma cikakken mahallin kalamansa ba.

Wannan ya sa ya zama dole a yi taka-tsantsan wajen yaɗa irin waɗannan kalamai, musamman ganin cewa Sheikh Gumi ya taɓa yin magana kan marigayi Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi bayan rasuwarsa a watan Afrilun 2025.

A lokacin, Sheikh Gumi ya bayyana cewa Dutsen Tanshi ya tsaya tsayin daka wajen tauhidi, tare da yi masa addu’ar Allah Ya gafarta masa, duk da cewa ya ambaci wasu kura-kurai da ya ce malamin ya aikata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments