Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciDangote: Na mallaki jirgin sama na kaina tun ina da shekara 22

Dangote: Na mallaki jirgin sama na kaina tun ina da shekara 22

Shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya mallaki jirgin sama na kashin kansa tun yana da shekaru 22 da rabi.

Shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya mallaki jirgin sama na kashin kansa tun yana da shekaru 22 da rabi.

Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da sayar da hannun jarin matatar Dangote da kamfanin petrochemicals ta hanyar IPO a Nigerian Exchange da ke Legas.

Ya ce duk da cewa ya ji daɗin rayuwarsa a matsayin ɗan kasuwa, yanzu ya fi son ganin masu hannu da shuni sun zuba dukiyarsu a harkokin da za su ƙara samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Dangote ya yi kira ga masu arziki da ke kashe makudan kuɗaɗe wajen mallakar jiragen sama masu tsada da su mayar da wani ɓangare na dukiyarsu wajen samar da kayayyaki da ayyukan yi.

Ya ce Najeriya ba za ta iya zama babbar ƙasa ta fuskar tattalin arziki ba tare da zuba jari a harkokin samarwa da sauran abubuwan da ke ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments