Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sake tunatar da maniyyatan Hajjin 2027 cewa wa’adin kammala rajista da shigar da bayanan da ake buƙata ya rage saura kwanaki 18.
NAHCON ta sanya ranar 26 ga Satumba 2026 a matsayin wa’adin ƙarshe na kammala aikin rajista da shigar da bayanan biometric na maniyyata a dandalin Nusuk-Masar da Saudiyya ta amince da shi.
Hukumar ta yi gargadin cewa rashin kammala matakan da ake buƙata cikin wa’adin da aka sanya na iya haifar da rasa gurbin aikin Hajjin da aka ware.
Yayin da wa’adin ke ƙara matsowa, NAHCON ta buƙaci maniyyatan da ba su kammala rajista ko biyan abin da ya rage ba da su gaggauta kammala dukkan matakan da ake buƙata.