Bayanan ‘yan sanda a jihar Maharashtra ta Indiya sun nuna cewa maza 383 ne suka kashe kansu a gundumar Jalgaon tsakanin Janairu da Yuni 2026.
Bincike ya nuna cewa dalilan sun haɗa da matsalolin iyali, basussuka, shaye-shaye da damuwar rayuwa. Daga cikin waɗanda suka mutu, 29 sun kashe kansu ne saboda rashin samun abokiyar aure.
Bayanan NFHS-5 sun kuma nuna cewa kusan kashi 30 cikin 100 na mazan Maharashtra masu shekaru 20 zuwa 49 ba su yi aure ba, yayin da adadin matan da ba su yi aure ba yake kusan kashi 11 cikin 100.
Wasu maza a Jalgaon sun ce rashin aikin gwamnati, rashin gida da ƙarancin kuɗi na sa iyalan mata ƙin amincewa da su. Wasu iyalai har suna gina gidaje ko sayen filaye domin ƙara wa ‘ya’yansu damar samun aure.
Masana sun ce matsalar tana da alaƙa da sauyin tattalin arziki, rashin aikin yi da kuma sauyin abubuwan da mata ke nema wajen zaɓar abokin aure.
Wata masaniya kan daidaiton jinsi, Darshana Pawar, ta ce bai dace a ɗora alhakin matsalar kacokan kan mata ba, domin buƙatun da suke nema kamar samun aiki, kwanciyar hankali da lokacin tattaunawa da abokin aure abubuwa ne na yau da kullum.
Masana sun kuma danganta ƙarancin mata da shekarun baya, lokacin da ake yawaitar zubar da cikin ‘ya’ya mata. Sun ce wannan na iya zama ɗaya daga cikin dalilan da ke haifar da rashin daidaiton adadin maza da mata a shekarun aure.