Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta shirya fitar da jerin sunayen ƴan takarar Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Tarayya na ƙarshe domin zaɓen 2027 a ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026.
Rahotanni sun ce matakin na daga cikin shirye-shiryen hukumar na tunkarar babban zaɓen da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairu, 2027, inda za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Tarayya a rana ɗaya.
INEC ta riga ta fitar da jerin sunayen ƴan takara na wucin-gadi, yayin da wa’adin sauya ko maye gurbin ƴan takarar Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ya ƙare ranar 22 ga Agusta.
Jam’iyyun siyasa kuma sun kammala gabatar da takardun ƴan takararsu a ranar 29 ga Agusta.
Fitar da jerin sunayen ƙarshe zai bayyana waɗanda INEC za ta amince da su a hukumance domin fafatawa a babban zaɓen 2027.
Hukumar ta kuma tanadi ranar 6 ga Fabrairu, 2027 domin gudanar da zaɓen gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi.