Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiAn harbe Bursar na jami’ar NOUN, Nasiru Marafa, har lahira

An harbe Bursar na jami’ar NOUN, Nasiru Marafa, har lahira

An harbe Bursar na Jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN), Nasiru Marafa, har lahira yayin da yake dawowa daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

An harbe Bursar na Jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN), Nasiru Marafa, har lahira yayin da yake dawowa daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Jami’ar ce ta sanar da rasuwarsa a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, wadda Magatakardar jami’ar kuma Sakataren Majalisar Gudanarwa, Oladipo Ajayi, ya sanya wa hannu.

Sai dai jami’ar ba ta bayyana inda aka harbe Marafa ba, ko kuma cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru.

NOUN ta bayyana Marafa a matsayin ma’aikaci mai jajircewa, wanda ya riƙe mukamai daban-daban na kula da jami’ar kafin daga bisani aka naɗa shi Bursar a watan Satumba na 2026.

Jami’ar ta ce mutuwarsa babban rashi ne ga al’ummar makarantar, inda ta aika da ta’aziyyarta ga iyalansa, ‘yan uwa, abokai da abokan aikinsa.

NOUN ta kuma ce za ta sanar da bayanan jana’izarsa da zarar iyalan mamacin sun fitar da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments