Mazauna garin Funtua a Jihar Katsina sun shiga cikin fargaba a daren Alhamis, bayan rahotannin cewa wasu ’yan bindiga sun zagaye wasu sassan garin tare da ruwan harbe-harbe.
Wasu mazauna garin sun shaidawa ICONIC TIMES cewa a halin yanzu suna cikin firgici tun bayan da suka fara jin karar harbe-harbe a wasu sassan garin a cikin daren, lamarin da ya sanya mutane da dama neman mafaka a gidajensu tare da takaita zirga-zirga.
Har ya zuwa yanzu ba a tabbatar da musabbabin harbe-harben ko kuma rasa rayuka ko aka yi garkuwa da su ba.
Haka kuma, babu wani bayani a hukumance daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ko wata hukumar tsaro dangane da lamarin zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Funtua na daga cikin yankunan Jihar Katsina da suka sha fama da hare-haren ’yan bindiga a baya, ciki har da yunkurin satar mutane da kuma hare-haren da jami’an tsaro suka dakile.