Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaPeter Obi da Kwankwaso sun gudanar da taron tattaunawa da al’umma a...

Peter Obi da Kwankwaso sun gudanar da taron tattaunawa da al’umma a Jihar Rivers

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da abokin takararsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun gudanar da taron tattaunawa da jama’a a birnin Fatakwal na Jihar Rivers.

Taron na daga cikin shirye-shiryen da ‘yan takarar ke gudanarwa domin tattaunawa da jama’a kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar da kuma makomar Najeriya.

Rahotanni sun ce taron ya mayar da hankali ne kan ra’ayoyin jama’a, ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta da kuma irin matakan da ake ganin za su taimaka wajen inganta rayuwar al’umma.

Haka kuma, ana sa ran taron zai ba jama’a damar bayyana damuwarsu da kuma gabatar da tambayoyi kan manufofin siyasa da shirin tafiyar NDC gabanin babban zaɓen 2027.

Peter Obi da Kwankwaso na daga cikin manyan ’yan siyasar da ke neman goyon bayan jama’a yayin da ake ƙara kusantar babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments