Kamfanin hada-hadar kuɗi na OPay Digital Services Limited ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan wani mai amfani da kafar X, bisa zargin yaɗa labarin ƙarya cewa kamfanin zai dakatar da ayyukansa daga 1 ga Satumba, 2026.
OPay ta bayyana labarin a matsayin ƙarya, yaudara da kuma ɓata suna, tana mai cewa saƙon ya haifar da illa ga martabar kamfanin da kasuwancinsa.
Kamfanin ya bukaci mai amfani da X mai suna Cute Hafserh (@haifah_er_abba) da ya goge saƙon, ya janye zargin da ya yi tare da ba kamfanin haƙuri.
A cikin wata sanarwa da Babban Lauyan OPay, Akinfolabi Rokosu, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, kamfanin ya ce an sanar da shi cewa an wallafa saƙon ne a ranar 30 ga Agusta, inda aka gargadi kwastomomin OPay da su cire kuɗaɗensu saboda wai kamfanin zai dakatar da ayyukansa na wani lokaci ba tare da bayyana ranar da zai dawo aiki ba.
OPay ta ce wannan ikirari ba shi da tushe, kuma ta bai wa mai wallafa saƙon wa’adin zuwa 11:59 na daren Litinin da ya goge saƙon tare da dakatar da sake yaɗa irin wannan bayani.
Kamfanin ya jaddada cewa ayyukansa suna gudana yadda ya kamata, kuma babu wani shirin dakatar da ayyukan OPay daga ranar 1 ga Satumba, 2026.