Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta yi wa mutane 150,346 allurar rigakafin cutar mashako cikin kwanaki biyar, a wani mataki na dakile yaɗuwar cutar a jihar.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Ibrahim Kaula Mohammed, ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Litinin.
Ya ce an fara aikin rigakafin ne a ranar 25 ga Agusta, a gundumomi 15 da ake ganin suna cikin haɗarin kamuwa da cutar a ƙananan hukumomin Bakori, Charanchi, Funtua, Mashi da Kankia.
Daga cikin wadanda aka yi wa rigakafin, mutane 99,036 masu shekaru 5 zuwa 15 sun karɓi rigakafin Tetanus-Diphtheria (Td), yayin da yara 51,310 suka karɓi Pentavalent.
Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne bayan rahoton bullar cutar a ƙananan hukumomi 29 daga cikin 34 na jihar, inda Funtua ke da mafi yawan adadin waɗanda ake zargi sun kamu.
Sanarwar ta ce gwamnati ta kuma samar da ƙarin allurai 650,000 na rigakafin mashako domin faɗaɗa aikin zuwa sauran wuraren da cutar ta shafa da kuma yankunan da ke cikin haɗari.
Haka kuma, an kafa ƙarin cibiyoyin killace marasa lafiya guda uku, yayin da ake ci gaba da aikin sa ido, gano waɗanda suka yi hulɗa da masu cutar, kula da marasa lafiya da wayar da kan al’umma.