Gwamnatin Tarayya ta amince da shirin haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu (PPP) na dala biliyan 1.295 domin mayar da Dam ɗin Challawa Gorge da ke Kano zuwa babbar cibiyar masana’antar noma ta zamani.
Hadejia Jama’are River Basin Development Authority (HJRBDA) ce ta sanar da amincewar a wata wasiƙa mai kwanan wata 18 ga Agusta 2026.
A ƙarƙashin shirin, kamfanin Al Qaryah Agro Allied Ltd zai bunkasa da sarrafa ayyukan noma da kiwo na zamani, ciki har da kiwon kifi, hydroponics, aquaponics, noman shinkafa da kifi tare da ban ruwa.
Hukumar ta ce kamfanin ne zai gudanar da ayyukan, amma gwamnatin tarayya za ta ci gaba da mallakar Dam ɗin da kuma kula da albarkatun ruwansa.
Shugaban kamfanin, Abubakar M. Nagwamatse, ya ce aikin zai samar da aƙalla guraben ayyukan yi 10,000 tare da ƙara samar da abinci da kuma buɗe damar fitar da amfanin gona zuwa ƙasashen waje.
Ya ce shirin zai haɗa da injin sarrafa abincin dabbobi mai ƙarfin samar da tan 150,000 a shekara da kuma wurin kyankyashe ƙananan kifaye guda miliyan 50.
Hukumar HJRBDA ta bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na amfani da albarkatun ruwa wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da abinci a Arewacin Najeriya.