Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce shi ne ɗan takarar da zai iya dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasar Najeriya.
Sowore ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, game da batun tallafin man fetur da kuma yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire shi.
A cewar Sowore, jam’iyyar AAC ta daɗe tana adawa da cire tallafin man fetur, kuma matsayinta bai taɓa sauyawa ba.
Ya zargi wasu ’yan siyasa da sauya matsayinsu kan tallafin saboda la’akari da siyasa, yana mai cewa bai kamata ’yan Najeriya su bari a sauya tarihin abin da ya faru kan wannan batu ba.
Sowore ya ce AAC ce kaɗai ta bayyana a fili cewa idan ta samu damar mulkar Najeriya, ba za ta cire tallafin man fetur ba.
Ya kuma yi zargin cewa Atiku ya sauya matsayinsa ne bayan AAC ta sake jaddada nata matsayi kan batun.
A nasa ɓangaren, Atiku Abubakar ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi wa ’yan Najeriya cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka ce an samu bayan cire tallafin man fetur.
Atiku ya ce gwamnati ta cire tallafin tare da buƙatar ’yan Najeriya su jure wahalhalun da matakin ya haifar, bisa alkawarin cewa za a yi amfani da kuɗaɗen wajen ayyukan ci gaba.
A gefe guda, Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta musanta zargin cewa gwamnatocin jihohi sun gaza bayyana yadda suka yi amfani da ƙarin kuɗaɗen da suka samu bayan cire tallafin.
Gwamnonin sun kuma nuna goyon baya ga faɗaɗa amfani da motocin CNG domin rage kuɗin sufuri da kuma sauƙaƙa wa ’yan Najeriya matsin tattalin arziki.