Tsohon kwamandan sojin Sabiya a Bosnia, Ratko Mladic, wanda aka samu da hannu a kisan kiyashin Musulman Bosnia, ya rasu yana da shekara 84.
Mladic ya mutu ne a ranar Alhamis yana tsare a birnin Hague, inda yake zaman gidan yari na Majalisar Ɗinkin Duniya. Lauyansa, Dragan Ivetic, ya tabbatar da rasuwar, sai dai bai bayyana dalilin mutuwarsa ba.
A shekarar 2017, an yanke wa Mladic hukuncin ɗaurin rai da rai bayan kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta same shi da hannu a laifukan yaƙi, cin zarafin bil’adama da kisan kiyashi.
An danganta Mladic da kisan kiyashin Srebrenica na shekarar 1995, inda aka kashe sama da Musulman Bosnia 8,000, galibinsu maza da yara. An bayyana kisan kiyashin a matsayin mafi muni da aka samu a Turai tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
Haka kuma, sojojin da Mladic ya jagoranta sun taka rawa wajen ƙawanyar Sarajevo tare da kai hare-hare kan fararen hula. An kuma samu rahotannin azabtar da fursunoni da wasu munanan laifuka a lokacin yaƙin Bosnia daga 1992 zuwa 1995.